fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Hukumar DSS ce ta kashe mutane 14 a jihar Imo kuma dukkansu masu laifi ne, Gwamna Uzodimma ya fadawa ‘yan jihars ta dake yin zanga zanga

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma yayi tsokaci kan zanga zangar da al’ummar Otulu keyi na cewa hukumar Ebubeagu ta kashe masu matasa 14 ba tare da aikata laifin komai ba.

A ranar litinin ne mutanen yankin suka gudanar da zanga zangar cewa matasan daga gidan biki suke dawowa amma aka bude masu wuta aka kashe su.

Yayin da shi kuma gwamnan jihar, Uzodimma ya bayyanawa manema labarai cewa hukumar ‘yan sanda sirri ta DSS ce ta hallaka matasan.

Inda ya kara da cewa gabadaya matasan masu laifi ne kuma hukumar ta kashe sune yayin data je farautar ‘yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published.