fbpx
Monday, June 27
Shadow

Hukumar DSS ta kama wani dan fashin da ya addabi al’ummar Ogun

Jami’an hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS), reshen jihar Ogun, sun cafke wani kasurgumin dan fashi da makami da ake zargi da yi wa al’ummar Ota ta’addanci a karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar.

Wanda ake zargin, Elijah Adeogun aka Killer, an kama shi ne da misalin karfe 2.25 na daren ranar Litinin, 16 ga watan Mayu, a unguwar Araromi Estate, Iyesi, Ota, biyo bayan takardar koke da iyalan Adelupo na Ipetu Baba Ode suka rubuta ta hanyar Iju-Ota.

A cewar jaridar Nigerian Tribune, koken ya kunshi zargin cewa Adeogun ne ke da alhakin kisan gillar da aka yi a ranar Litinin 17 ga watan Nuwamba, 2021, kan wani lamari na fili tare da wasu mutane shida.

Karanta wannan  An damke mutumin daya kashe wata mata mai yara biyu a jihar Anambra

An ci gaba da cewa, wata tawagar dabara ta rundunar ta gudanar da wani samame na musamman wanda ya kai ga cafke Adeogun tare da wani Oyelekan Okunade.

A halin yanzu za a mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike na musamman.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.