fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Hukumar EFCC ta kama mutane 11 da ake zargi da damfara ta intanet a Auchi

Jami’an Ofishin shiyyar Benin na hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’anci, EFCC sun kama wasu mutane 11 da ake zargi da damfara ta intanet.

Wadanda ake zargin sun hada da David Martins, Shegun Elijah, Abagolu Samson, Peter Emmanuel, Emmanuel Noble, Timothy Johnson, Omo-Ogbebor Uyioghosa, Ibrahim Mohammed, Mavis Bello, Emmanuel Chibozie, da Ayiboye Alade, an kamasu a yau, Litinin, 22 ga Fabrairu, a Auchi, Jihar Edo.

Kayayyakin da aka kwato daga wadanda ake zargin sun hada da kwamfutocin tafi-da-gidanka, wayoyin hannu, da kuma wata mota kirar Toyota Camry.

A cewar Hukumar EFCC, wadanda ake zargin sun yi bayanai masu amfani kuma za a gurfanar da su a kotu da zaran an kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *