Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), reshen jihar Kwara, ta kama wani matashi dan shekara 30 da ake zargi da damfarar Sarkin Okuta a Jihar Kwara, Idris Abubakar, kudi N33,399,999.
A cikin wata sanarwa da kakakin ta, Wilson Uwujaren ya fitar, EFCC ta ce wanda ake zargin mai suna Fidelis Poor, ya gamsar da basaraken cewa ya na da kwantenan kaya da zai taimaka wajen ci gaban al’umma.
A cewar EFCC, wanda ake zargin ya shaida wa sarkin, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne, cewa kwantena na jiran izini a Abuja, kuma ya bukaci sarkin gargajiya ya biya wasu kudi domin a sako kwantenan.
Za’a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya a karshen binciken, inda ya kara da cewa ana ci gaba da kama wasu ‘yan kungiyar.