Kwamandan hukumar farar hula, Ahmad Audi ya bayyana cewa zasu dauki Abimiku Abraham, wato yarinyar shugabansu wanda ya rasa ransa a harin kurkukun Kuje.
Ilyasu Abraham ya mutu ne a ranar biyar ga watan Yuli yayin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai hari gidan kurkuku na Kuje dake babban birnin tarayya.
Wanda a jiya hukumar ta baiwa iayalansa naira miliyan 2.8 kuma tayi masu albishir cewa zata dauki ‘yarsa aiki a sabbin ma’aikatan da zata dauka na gaba.