Mukaddashin kwanturola a sashin aiyukan gwamnatin tarayya, Mista Usman Yahaya ya ce a cikin watanni biyu da suka gabata, rundunar ta cafke kwantena 15 na magungunan jabu da wadanda lokutan amfani dasu ya kare da kuma wasu haramtattun kayayyaki a jihar Legas.
Hakanan Kwanturolan hukumar Ya nuna matukar damuwa kan ayyukan wasu bata gari masu shigo da kaya ta tashar jirgin ruwa, da kuma masu fasa-kwaurin wadanda ya ce sun dauki sabbin dabaru kuma a koyaushe suna barazana ga rayukan al’umma sakamakon kin yin abin da ya dace.