Hukumar FCTA ta jihar Abuja ta kama mutane biyu dake sayar da lalataccen naman kaza a kasuwar Garki.
Inda shugaban kungiyar Kaka Bello ya bayyana cewa sun kama su ne bayan da hukumar dake lura da kasuwar ta kawo masu wannan korafin.
Kuma sun garzaya sun kamo su amma mutanen sun rigada sun dauke lalataccen naman daga kawuwar kafin hukumar ta kama su.
Inda hukumar tace tana cigaba da bincike domin tabbatar da cewa an zubar da naman ba wata kasuwar aka kai shi ba, sannan daga karshe zata maka su a kotu.