Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta bayyana cafke wasu mutum 79 da aka samu da laifin sabawa dokokin hanya tsakanin watan Disamba zuwa 24 ga watan a jihar Akwa Ibom.
Kwamandan sashin hukumar FRSC dake jihar Akwa Ibom, Mista Oga Ochi, shine ya bayyana hakan a wata hira da yayi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Uyo ranar Lahadi.
Ochi ya ce an kama masu laifin ne saboda laifuffukan da suka hada da yin lodi fiye da kima, tuki da tsofaffin tayoyi, tuki ba tare da lasisin tuki ba, tare da takardun mota na bogi.
A cewarsa, tuni masu laifin da aka kama sun biya tara kamar yadda doka ta tanada.