fbpx
Friday, February 26
Shadow

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta gano wani sito ajiye da tabar wiwi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta yi nasarar gano wani sito makare da tabar wiwi a garin, Fatakwal dake jihar Ribas.

Hukumar ta NDLEA, ta shaida hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta bayyana cewa ta yi nasarar kame kayan ne sakamakon wasu bayanan sirri da hukumar ta samu.

Hukumar ta kara da cewa jami’anta sun kutsa kai cikin rumbun ajiyar kayan mayan ne da safiyar ranar Asabar 20 ga watan Fabrairun shekarar 2021 inda suka gano wasu buhu 23 na buhunan tabar wiwi masu nauyin kilogram 621 da hodar iblis mai nauyin 0.029kg.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *