fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta horar da Jami’anta Dabarun kare kai

Kungiyar Karate ta jihar kano ta baiwa Jami’an hukumar Hisba 200 horo na dabarun kare kai daga abokan gaba.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da Kakakin Hukumar Lawal Ibrahim-Fagge ya fitar a ranar Alhamis.

Kwamandan hukumar Hisba ta jihar Kano Harun Ibn sina, ya matukar yabawa da horon da a ka baiwa Jami’an sa, ya kuma Kara da cewa daman horon ya zama wajubi ga Jami’an kasancewar su ba makami su ke rikewa ba.

Haka zalika kwamandan Ya kara da cewa “irin wannan horon zai taimaka musu wajen kare kansu idan an kai musu hari.

Karanta wannan  'Yan bindiga sun kashe dan sanda sunyi garkuwa da dan kasar Sin a jihar Kwara

Horan da kungiyar ta baiwa Jami’an ya hada da gudun tsere, dabarun kare kai gami da yadda mutum guda zai iya tunkarar mutane uku shi kadai.

Hakanan an kuma koyawa Jami’an yadda a ke fasa Bulo da hannu, tare da sauran wasu dabaru.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.