fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Hukumar Hisba ta lalata kwalaben giya 3000 a Jigawa

Hukumar Hisba ta jihar Jigawa ta lalata kwalaben giya 3000 da aka kwace a karamar hukumar Kazaure.

Kwamandan karamar hukumar Malam Bello Musa Kazaure ya bayyana hakan bayan lalata giyar a Kazaure.
Ya ce wannan matakin ya yi daidai da kokarin da rundunar ke yi na magance mummunar dabi’a da munanan halaye a tsakanin al’umma.
Bello ya ce an kwace kwalaban giyar ne daga wasu gurare da ke garin Kazaure.
Ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kamawa da gurfanar da duk wani mai siyar ko siyan giya a cikin Jihar.
Ya ce wannan shi ne atisaye na biyar da jami’an rundunar ke gudanar wa a yankin don rage kaifin gani da ido a yankin.
Bello ya lura cewa sha da sayar da giya sun kasance haramtattu a cikin jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan bindiga sun kashe dan sanda sunyi garkuwa da dan kasar Sin a jihar Kwara

Leave a Reply

Your email address will not be published.