fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hukumar Hisbah ta kama karuwai 32, 12 daga ciki an tabbatar da suna ɗauke da ƙwayar cutar Kanjamau

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wasu karuwai har guda 32 wadanda 12 daga ciki aka tabbatar sa suna dauke da cutar kanjamau.

Kwamandan Hisba na jihar Muhammad Harun Ibn Sina shine ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar kano.

Muhammad Harun ya bayyana cewa, an kama karuwanne a wani sumame da hukumar ta kai a wata kusuwa dake Badume a karamar hukumar Bichi.

A cewarsa, kamen wanda hadin gwaiwa ne da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshan jihar kano.

Ya kara da cewa a yayin sumamen, jami’an hukumar sun kama wata mata da ta kware a harkar sayar da kwaroron roba da kuma wasu maza tara da ke sayar da kwayoyi.

Hakanan kwamanda ya shaida cewa, karuwan da hukumomin suka cafke galibin su sun fito ne daga jihohin Edo, Anambra, Adamawa, Enugu, Zamfara, Katsina, Kuros Riba, Jigawa, da kuma Jamhuriyar Kamaru.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.