fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Hukumar INEC ba zata amince da dan takarar da baiyi zaben fidda gwani a jam’iyyarsa ba

Hukumar zabe ta kasa watau INEC ta bayyana cewa ba zata amince da wani takarar da baiyi zaben fidda gwani ba a jam’iyyarsa.

Fetus Okoye, babban kwamishinan hukumar ne ya bayyana hakan yayin daya ke ganawa da manema labarai na Channels.

Inda yace a kudin tsarin mulkin Najeriya ba inda aka ce hukumar zabe ta amince da dan takarar da baiyi zaben fidda gwani a jam’iyyarsa ba.

Kuma yace dan takarar da taki amincewa dashi shi din yanada damar da zai iya makata a kotu idan bai gamsu da abinda suka fada masa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.