fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Hukumar INEC ta dakatar da sabunta rigistar katin zabe a jihar Imo, biyo bayan kashe mata ma’aikaci da yan da yan bindiga sukayi

Yan bindiga sun kai hari kasuwar Nkow Ihitte dake karamar hukumar Ubom a jihar Imo, inda suka kashe ma’aikacin hukumar zaben Najeriya ta INEC da wani mutun guda.

Yan bindigar sun kai hari ne yayin da hukumar ke sabuntawa yan karamar hukumar katin zaben su, inda suka bude masu wuta a kauyen.

Kuma hukumar INEC ta bayyana cewa ta dakatar da yin rigistar zabe a jihar yayin da kuma ta mika sakon ta’aziyya ga yan uwan ma’aikacin nasu da aka kashe, kuma tasha alwashin nemo sauran ma’aikatan nata guda biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.