Hukumar KAROTA dake jihar Kano ta cafke wasu kayayyaki da hukumar ke zargin magun-guna ne da basu da rijista.
Kakakin hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa shine ya sanar da hakan ga manema labarai a jihar Kano.
A cewara anyi Nasarar cafke motar dakun kayana ne da misalin karfe 3 na dare a kan titin Igbo road dake sabon gari a karamar hukumar Fagge.
Da yake magana kan wadanda su ka daukko dakon kayan ya ce tuni sun ka tsere.