Rundunar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Jigawa (FRSC), ta ce ta tura jami’ai 356 domin tabbatar da tsaron lafiyar masu ababen hawa da sauran masu amfani da titin yayin hutun Eid-el-Kabir a jihar.
Mista Ado Adamu, kakakin hukumar FRSC a jihar, shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a Dutse ranar Alhamis.

Rundunar ta ce, jami’an da aka tura sun hada da ofisoshi 89, da kuma mashals 267 da kuma mashals na musamman 1000.
Kwamandan ya ce an kuma tattara motocin sintiri guda bakwai da motocin daukar marasa lafiya guda uku don yin sintiri na Musamman kwana 10 na Sallah, wanda zai fara a ranar 29 ga Yuli.
Ya yi gargadin cewa: “Hukumar FRSC a shirye take ta kama direbobi da direbobin babura da aka same su da keta ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa kafin, lokacin, da kuma bayan bikin,” in ji shi.