fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Hukumar Kiyaye Hadura FRSC ta bukaci masu Ababan hawa da su lura da Dokokin Hanya

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta shawarci masu ababen hawa da su yi biyayya ga dokokin hanya domin kauce wa hadurra a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Kwamandar sashin hukumar FRSC dake jihar Ebonyi, Misis Stella Uchegbu, ce ta ba da shawarar a ranar Asabar a lokacin da ‘take fadakar da mutane sanin muhimmancin kiyaye dokokin hanya musamman a lokatan karshan shekara.

Uchegbu ta ce watannin karshan shekara lokuta ne da wasu masu ababan hawa ke amfani dashi wajan yin tukin ganganci Wanda hakan ke zama barazana ga rayuwar mutane da su kansu dirobin.

A karshe ta bukaci da masu Ababan hawa su lura tare da yin biyayya da Dokokin hanya Dan kaucewa fadawa cikin Nadama.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.