by Abubakar Saddiq
Hukumar Kiyaye hadura ta kasa reshan jihar Enugu ta aike da sakon gargadi ga Direbobi kan kaucewa gudun ganganci a sabuwar shekarar 2021 da muke ciki.
Kwamandan hukumar Mista Kalu Ogbonnaya shine ya bayyana hakan ga Manema labarai a jihar, inda ya ce mafiya yawan haduran da ke afkuwa a jahar yana da nasaba da gugun ganganci.
Hakanan kwamandan ya gargadi Direbobi da su kaucewa shan muggan kwayoyi a yayin da suke kan tuki inda ya ce hakan na haifar da hadura a kan hanyoyi.