Hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC tayi gargadin matuka da su kaucewa shan kwayoyi ko abubuwan dake saka maye a yayin da suke tuki domin kaucewa hadura a lukutan da suke gudanar da bukukuwan ranar Masoya.
Jami’in hulda da Jama’a na hukumar Bisi Kazeem, shine yayi wannan jan kunnan a ranar Lahadi A babban birnin tarayya Abuja.