fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa zata fara rijistar aikin Hajji na shekarar 2021

NAHCON za ta fara rijistar aikin Hajji na shekarar 2021 Nan da wata mai kamawa

 
Shugaban, Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON), Mista Zikrullah Hassan, ya ba da sanarwar cewa a ranar 9 ga Satumban bana, shine zai zama a matsayin ranar da za a fara rajistar masu niyyar aikin hajji na shekarar 2021.
 
Hassan, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake karin haske ga manema labarai a Abuja, ya ce hukumar za ta bude shafukanta domin saukakawa maniyyata yin rajistar.
 
Ya kuma shawarci mahajjata da su adana ajiyar kudaden su ga  hukumar har zuwa shekarar 2021.
Idan zaku tuna Hukumar kasar Saudiya ta dakatar da aikin hajjin bana ga masu ziyartar aikin hajjin a wannan shekara ta 2020 a sakamakon bullar cutar Coronavirus.
 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Fusatattun matasa sun babbaka mutane biyu da suka yiwa yarinya fyade har suka kasheta a jihar Enugu

Leave a Reply

Your email address will not be published.