Hukumar kula da bayanai ta Najeriya dake da hadakar kwararrun manazarta bayanai sun baiwa shugaban hukumar kula da cigaban fasahar sadarwa ta zamani ta Najeriya, NITDA a takaice, watau Sheikh Isah Aliyu Pantami damar zama daya daga cikin membobinsu na girmamawa.