Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Saudiyya (SFDA) ta ƙwace tan biyar na naman kajin da ya lallace a wani gidan ajiye kayyakin abinci da ke birnin Riyadh.
Hukumar ta tabbatar da cewa gidan ajiyar kayan abincin ya saɓa wa ƙa’idoji masu yaw, cikin har da yin ƙarya sayar da kayayyakin da suka lalace, inda ake sake wa naman kajin mazubi tare da sanya musu sabbin kwanan watan lalacewa.
Haka kuma hukumar ta ce gidan ajiyar ya saɓa wa dokokin lafiya, da amfani da ma’aikatan da ba su da takardun shaidar karatun lafiya.
SFDA ta kuma rufe gidan ajiyar tare da lalata duk kayyakin da ta ƙwace.