Hukumar Fasakauri ta Kasa ta cafke wasu tarun katan-katan na kayayyaki da suka hada da jabun magun-guna Wadanda a kai fasakaurin su daga kasar Indiya da kudin su ya kai kimanin Naira Miliyan N869.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Jerry Attah, ya sanya wa hannu, a ranar Litinin, wanda aka rabawa manema labarai, rundunar ta ce kayayyakin da aka kama sun hada Buhunan shinkafa, sabulai, jabun Magun-guna da sauran su.
Hukumar ta sha Al’washin cigaba da kame kayayyakin da suka saba doka kamar yadda dokar hukumar ta tanada.