kwastam ta kwace shinkafa da wake da ya kai kimanin na naira miliyan 12.7 a jihar Kano
Hukumar wacce ke aikin tabbatar da doka dake tsakanin kano da Jigawa ta NCS tayi ram da wasu masu fasa kauri a jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Isa Danbaba ne ya sanar da haka inda ya ce ranar 15 ga Afrilu, ma’aikatan hukumar suka cafke wata motar ɗaukar kaya da aka yi mata lodin buhunan shinakfa ‘yar waje guda 295, kowane buhu yana da nauyin kilogiram 50 da aka ɓoye su a ƙarƙashin wasu buhuhunan wake guda 351.
A cewar sa jimlar adadin kudin shinkafar da aka ƙwace ya kai N6,603,870, yayin da na wake ya kai N6,000,741. Jimillar kuɗaɗen kayan da aka ƙwace su ne N12,704,611”
Hukumar ta gargadi masu fasa kauri da cewa hukumar a shirye take da susa ƙafar wando ɗaya da masu kunnen ƙashi.