fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Hukumar LFP zata haramtawa Neymar wasanni bakwai

Alkalin wasa ya baiwa Neymar jan kati yayin da suke karawa da Marseille bayan na’urar VAR ta bayyana cewa Neymar ya naushi Alvaro saboda ya cin zarafin shi bayan da ya suffanta dan wasan Brazil din da kalmar biri.

Hukumar wasannin kasar Faransa LFP zata gudanar da bincike akan lamarin kafin ta yankewa Neymar hukunci, kuma hukumar ta bayyana cewa zata dakatar da Neymar daga buga wasanni har guda bakwai a cewar RMC Sport. Shima Alvaro za’a dakatar da shi daga buga wasanni 10 idan har aka kama shi da laifi akan wannan lamarin.
Yan wasan sun cigaba da mayarwa junan su martani a kafafen sada zumunta yayin da Alvaro yake cewa Neymar marar nasara, shi kuma Neymar yace rashin nasara tana daya daga cikin harkar wasa amma shi ba zai taba amincewa da zagi ba ko cin zarafi.
Kungiyar Marseille ne suka yi nasarar cin Paris Saint German 1-0 a wasan wanda aka baiwa yan wasan PSG har guda biyar jan kati kuma aka ba wasu yan wasa 12 yalan kati.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *