fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Hukumar NAFDAC ta haramta yin amfani da wani man kai da ake sarrafawa a Nahiyar Turai

Hukumar NAFDAC ta Najeriya ta bayyana cewa ta samu sako daga Hukunmar RAPEX ta nahiyar turai, cewa an haramta amfani da man kai da suke sarrafawa mai suna Placentyne Hair Lotion.

Darekta janar na hukumar ne ya rattaba hannu a wasikar da aka turo Najeriya, inda aka mikawa manema labarai na NAN suka wallafa.

Hukumar tace man kan na dauke na wani sinadri ne na Methylchloroisothiazolinone da kuma Methylisothiazolinone (MCI and MI), kuma an haramta yin amfani dasu wurin sarrafa man kan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.