fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Hukumar NAPTIP ta ceto mutane 65 da akayi safarar su a Jamhuriyar Nijar

Hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP), ta ce ta ceto mutane 65 da aka zargin anyi safarar su a Jamhuriyar Nijar.

Kwamandan shiyyar NAPTIP mai kula da Kano, Mista Abdullahi Babale, ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Kano.

Ya ce jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa da na ‘yan sandan Najeriya ne suka kama wadanda lamarin ya rutsa da su a mashigin shiga Kongolam da ke jihar Katsina a kan iyakar Najeriya da Nijar.

Babale ya ce wadanda abin ya shafa ‘yan Najeriya ne da suka hada da maza 17 da mata 48 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 42.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wadanda abin ya shafa sun fito ne daga Ekiti; Ondo, Osun, Oyo, Lagos, Abia, Edo, Cross-River, Delta, Imo, Rivers, Akwa Ibom, Ogun da Enugu.

Ko’odinetan ya ce wadanda harin ya rutsa da su na tafiya ne ta hanyar Libya zuwa Italiya da Kanada da sauran sassan Turai domin yin lalata da su.

Ya ce hukumar ta shiga zurfafa bincike a kan lamarin domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya, tare da hada wadanda abin ya shafa da iyayensu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.