Hukumar kula da harkokin Lafiya ta Najariya, NCDC ta bayyana cewa, cutar Marbug Virus data bulla a kasar Ghana ka iya shigowa Najariya.
Hukumar tace lura da kusancin da Najariya ke da kwai da kasar Ghana ya nuna cewa cikin sauki cutar zata iya shigowa Najariya.
Dan hakane take kira ga mutane da su je a musu gwajin cutar dan kare kawunansu.
Cutar dai ta kama tare da kashe wasu mutane 2 a kasar ta Ghana.
Jami’in hukumar NCDC, Ifedayo Adetifa ya bayyana cewa, suna saka ido sosai kan yiyuwar ballewar wannan cuta a Najeriya.