Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta cafke wani mai suna Ukaegbu Onyekachi, da laifin safarar hodar iblis.
An kame Onyekachi ne a ranar Talata a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, a cewar Ahmadu Garba, wani babban jami’in hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi.
Ya tabbatar da cewa an cafke wanda ake zargin ne da kilogram 3.30 na miyagun kwayoyin a lokacin da fasinjojin fasinjojin jirgin na Ethiopian suka shigo ciki a zauren E-airport na filin jirgin.
Garba, wanda shi ne kwamandan NDLEA a filin jirgin, ya bayyana cewa Onyekachi ya iso Najeriya ne a jirgin Ethiopian Airways daga Sao Paulo na Brazil zuwa Addis Ababa.
Ya bayyana cewa miyagun kwayoyin an boye su ne a cikin kwalayen riguna, Inda nan take aka damke wanda ake zargin.