fbpx
Monday, August 8
Shadow

Hukumar NDLEA ta cafke wasu mutane 70 da ake zargi a Kano

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce ta cafke wasu mutane 70 da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne tare da kame kilogram 1,537.472 na haramtattun kayan maye a jihar Kano a watan Nuwamba.

Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Kano, Ibrahim Abdul, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a Kano ranar Talata.

A cewarsa, a  watan da ake ciki, rundunar a jihar Kano ta yanke hukunci a kan wasu mutane 16 da ake zargi yayin da wasu ke ci gaba da fuskantar shari’a.

Ya kuma yi kira ga jama’a, musamman shugabanin gargajiya, dana addinia da shugabannin al’umma da su ci gaba da bai wa rundunar ‘yan sanda goyon baya yadda ya kamata domin kakkbe mata gari a cikin al’umma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.