fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Hukumar NDLEA ta gargaɗi maniyyatan Aikin Hajji

Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya wato NDLEA ta gargaɗi mahajjata kan safarar miyagun ƙwayoyi.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito wata jami’ar hukumar Habiba Zubair a yayin da take gargaɗi a birnin Illori na Jihar Kwara a yayin da take jawabi ga mahajjatan bana.

Ta yi gargaɗin cewa magungunan da likitoci suka bayar da izinin sha kaɗai za a iya tafiya da su inda ta ce duk wani abu koma bayan hakan gwamnatin Saudiyya ba za ta lamunta ba.

Karanta wannan  'Yan sanda sun damke wasu 'yan Najeriya a kasar UK da laifin sayar da sassan jikin dan adam

Haka kuma ta yi gargaɗin cewa kada mahajaccin da ya kuskura ya karɓi kayan wani ajiya ko riƙo sakamakon za a iya ɓoye wasu abubuwan da aka haramta a cikinsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.