Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce har yanzu ba ta ci gaba da daukar aikin da ta dakatar ba bisa ka’idojin da kwamitin shugaban kasa kan yaki da Annobar cutar Covid-19 ta kindaya.
Shugaban sashen hulda da jama’a na NDLEA, Jonah Achema, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a da ya fitar, ya yi kira da ‘yan Najeriya su kula da shafukan ‘yan damfara