fbpx
Monday, March 1
Shadow

Hukumar NDLEA ta kai samame kananan hukumomi 3 a Jigawa, inda ta kama mutane 36

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Jigawa, ta ce ta cafke wasu mutane 36 da ake zargi daga Kananan Hukumomi uku na jihar cikin kwanaki biyu.
Hajiya Maryam Gambo, Kwamandan hukumar, ta bayyana a cikin wata sanarwa a Dutse ranar Juma’a cewa an kama wadanda ake zargin tsakanin Fabrairu 15 zuwa 27 ga Fabrairu, a Kirikasamma, Guri da Hadejia.
Gambo ta ce an kamasu ne a kasuwanni, shaguna da sauran wuraren buya, a kokarin da ake na kawar da saida haramtacciyar hanya da kuma shan muggan kwayoyi.
Ta bayyana cewa an kwato nau’ikan miyagun kwayoyi, wadanda suka hada da wiwi da kuma abubuwan da suke shafi tunanin mutum daga wadanda ake zargin.
Ta Kara da cewa za a sanya wadanda aka kaman a tsarin gyaran hali kuma ta gargadi mutane da su guji shiga harkar sha da saida miyagun kwayoyi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *