- Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta ce ta kama wasu mata biyu masu ciki a filin jirgin sama na Murtala Muhammed suna shirin safarar haramtattun ƙwayoyi.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce a ranar Laraba, 4 ga watan Mayu an kama wasu katan-katan na kwalaben giya da ake zargin suna ƙunshe da haramtattun ƙwayoyi, inda nan take aka kama wadda ta kai kayan don aikawa da su Dubai mai suna Shola Ogunrinde.
Ci gaban bincike ya sa aka kama wata mace mai ciki mai suna Seun Babatunde, waddda ke gudanar da harkokin sayar da kayan maye a Iyana da ke Legas, in ji NDLEA.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama mai ciki ta biyun ne mai suna Gloria Asibor ranar Alhamis, 5 ga watan na Mayu lokacin da take ƙoƙarin shiga jirgin Turkish Airlines zuwa Bolonia na Spaniya ɗauke da ƙwayar Tramadol 300 mai nauyin 200 da 225 giram.
A gefe guda kuma, an kama wani mai suna Nworie Phillip Chikwendu bayan ya dawo daga Brazil ranar Talata, 3 ga watan Mayu a jirgin Qatar Airways.
Sanarwar ta ƙara da cewa binciken da jami’ai suka gudanar ya sa suka gano fakitin hodar ibilis biyu a jakarsa ta baya ƙunshe cikin takalman silifa. Bayan an matsa da bincike ne kuma aka sake gano wasu fakiti biyu na koken ɗin.