fbpx
Monday, March 1
Shadow

Hukumar NEMA Ta Musanta Korar Ma’aikata 48

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa ta musanta korar ma’aikata 48.
An ruwaito a baya cewa NEMA ta dauki ma’aikata 48, amma ta sallame su bayan shekara guda da fara aikin.
Jami’in hulda da jama’a na NEMA, Manzo Ezekiel, a wata sanarwa da ya fitar a jiya, ya ce duk da cewa an dauke su aiki, amma ba a kore su ba.
Ya ce NEMA ta “soke” daukar ma’aikatan don rashin bin “ka’idojin da aka gindaya don daukar ma’aikatan gwamnati.”
Ezekiel ya taba shaidawa Aminiya cewa bai san da daukar ba.
Ya ce duk da cewa an samu amincewar daga Hukumar NEMA ta Gwamnati don daukar ma’aikata a shekarar 2018, amma ba a samu amincewar daga Ofishin Shugaban Ma’aikatan Tarayya da na Ma’aikatar Harkokin Jin Kai ba.
“Game da zargin cewa ba a biya albashin wadannan da aka dauka ba na shekara guda, dole ne a sake bayyana karara cewa NEMA ba ta biyan albashin Ma’aikatan Gwamnati,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *