fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Hukumar NSCDC ta cafke mutum 28 bisa zargin fasa bututun mai, a Abia

Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC), reshen Abia, tace ta cafke mutane 28 da ake zargi da laifin fasa bututun mai da lalata kayan gwamnati ba bisa ka’ida ba daga watan Satumba zuwa yau a jihar.

Kwamandan, hukumar Vincent Ogu, shi ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da manema labarai a Umuahia ranar Talata.

Ya ce, 20 daga cikin wadanda ake zargin tuni an gurfanar da su a gaban kotu.

Mista Ogu ya ce sauran takwas din, ciki har da hudu da aka kama a ranar Juma’a, ana kan gudanar da bincike a kansu kuma za a gurfanar da su nan gaba kadan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.