fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas, NEDC ta tallafawa Manoma da irin Shinkafa, Takin zamani da sauran kayan noma a jihar Bauchi

Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) ta ba da gudummawar kayayyakin gona, da suka hada da irin shinkafa, takin zamani, maganin ciyawa da kayan gwari ga kananan manoma domin bunkasa karfin samar da su da kuma inganta rayuwar su a jihar ta Bauchi.
Da yake jawabi a lokacin rabon kayayyakin, Manajan Daraktan NEDC, Mohammed Alkali, ya ce hukumar na shirin fara hada-hadar ayyukan gona da suka hada da samar da injunan noma da kayan aiki, iri, takin zamani, sinadaran gona da sauran kayan aiki don inganta samarwar karfin kananan manoma a yankin Arewa maso Gabas tare da basu damar inganta rayuwar su.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya gode wa NEDC kan wannan karimci sannan ya roke su da su tallafawa gwamnatin jihar wajen horar da ma’aikatan fadada da nufin ilimantar da kuma karfafa gwiwar manoma a jihar.
Gwamnan ya yaba wa NEDC game da saka hannun da take yi a jihar, ya kara da cewa ingantattun irin shinkafar da aka bayar za ta matukar inganta noman na su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *