fbpx
Friday, June 9
Shadow

Hukumar Soji ta kori janar dinnan da shekarar data gabata ya shiga Badakalar Miliyan 100

Kotun Hukumar sojin Najeriya ta kori Majo Janar Hakeem Oladapo Otiki dake kula da rundunar sojin Sokoto daga aiki bayan ta sameshi da laifin almundahanar kudi.

 

Kotun tace za’a ragewa sojan Mukami daga Majo Janar zuwa Birgedia Janar inda za’a kuma koreshi aiki ta hanyar wulakanci da kaskanci.

Saidai ai majalisar Koli ta sojin ta duba wannan hukunci dan tabbatar da shi ko kuwa akasin haka.

 

Hukuncin ya bukaci kudi Miliyan 135, da kudi dala 6,600, da kuma Miliyan 159 da aka kwato daga hannun janar din sojin duk a mayarwa da Hukumar Sojinsu.

 

Saidai Lauyansa, Bar. Israel Olorundare(SAN) ya bukaci a wa wanda yake wakilta sassauci.

 

Yace kamin yanzu Janar Otiki ya kasance hazikin soja da ya samu nasarori da dama a ayyukan da yawa hukumar sojin sannan kuma shine ke samarwa da iyalansa Abinci kuma bashi da lafiya ga matarshi ma tana da ciwon daji sannan mahaifiyarshi ta rasu shekarar data gabata.

 

Ya kara bada hujjar Janar dinne fa ya kwarmata maganar satar kudin da sojojin da ya aika suka yi a kaduna sannan kuma shine dai yayi yanda yayi ya samo kudin Naira Miliyan 100 ya mayarwa hukumar sojin sannan Miliyan 150 da ake magana akanta kudin aiki ne wanda yanzu haka ana kan gudanar da iki yayin da wasu tuni aka kammalasu.

 

Ya kara da cewa dan haka basu yadda da wannan hukunci ba zasu nemi a sake dubashi, lura da cewa a wanan shekarar ne ma Janar Otiki zai yi ritaya bayan shafe shekaru 45 yanawa Najeriya bauta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *