Sunday, May 31
Shadow

Hukumar sojojin Najeriya ta gano sojojin da suka zazzagi Buratai kuma za’a musu horon canja Hali

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa ta gano sojojin da suka zagi shugaban sojin Najeriya, Janar Tukur Yusugmf Buratai.

 

Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin sun zagi Buratai da Hukumar sojine yayin da mayakan Boko Haram suka kai musu harin kwantan bauna da ya tarwatsa motocinsu har sojoji 2 suka rasa ransu, wasu 3 suka jikkata.

Hutudole ya kawo muku labarin dazu inda Aka ga Sojojin Na kuka suma caccakar hukumar soji da Buratai

 

Harin dai yayi sanadin kashe mayakan Boko Haram 3 inda wasu suka tsere da harbin bindiga a jikinsu. Sanarwar tace duk da yake cewa a bakin daga irin abinda sojojin suka yi dama ana tsammaninshi, za’a yi kokarin yi musu Horo dan kawar musu fargabar da suka fuskanta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *