Sunday, July 21
Shadow

Hukumar Wutar lantarki ta Abuja zata yankewa hedikwatar Sojoji dana ‘yansanda wuta saboda bashi

Hukumar wutar lantarki ta Abuja ta bayyana cewa, zata yankewa manyan ma’aikatu da yawa wuta saboda bashin kudin wutar da ake binsu.

Ta bayyana cewa, daga cikin hukumin da ake bin bashin akwai hukumar sojojin, dana ‘yansanda da ma’aikatar mata ta tarayya, da jihar Kogi, da ma’aikatar Ilimi, da ma’aikatar masana’antu.

Hukumar tace ba wata ma’aikata da zata dagawa kafa zata yanke mata wuta.

Hakan na kunshene a cikin sanarwar da hukumar wutar ta fitar.

Karanta Wannan  "Mataimakin Gwamna A Najeriya Kamar Ba Ka Da Aiki Ne" -- Tsohon Mataimakin Gwamna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *