fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Hukumar Yaki Da Cin Hanci A Jihar Kano Za Ta Cigaba Da Tuhumar Tsohon Sarkin Kano Sanusi II

Hukumar sauraron koke da yaki da rashawa ta jihar Kano ta ce za ta ci gaba da bincike a kan tubabben sarkin Kano kamar yadda Kamfanin Dillacin Labarai NAN ya ruwaito.

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano ta hana hukumar bincikar tubabben sarkin a kan zarginsa da ake da damfara.

 

Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Rimingado ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya Talata, cewa ana ci gaba da bincike.

 

Hukumar sauraron koke da yaki da rashawa ta jihar Kano ta ce za ta ci gaba da bincike a kan tubabben sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, bayan umarni daga kotu.

 

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano ta hana hukumar bincikar tubabben sarkin a kan zarginsa da ake da damfarar naira biliyan 2.2.

 

Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Rimingado ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya Talata, cewa ana ci gaba da bincike.

Karanta wannan  Mutane miliyan daya muka kashe domin a samu zaman lafiya a Najeriya, cewar shugaba Buhari

 

“Ko a ranar Litinin hukumar ta gayyaci wasu kamfanoni kuma duk sun zo. Amma kuma za a ci gaba da bincikar tubabben sarkin bayan umarni daga kotu,” Rimingado yace.

 

Yace tube sarkin zai sa hukumar ta samu damar yin bincike ba tare da wani katsalandan ba ko wani shinge.

 

“A halin yanzu muna da sararin bincike tunda babu sarkin a kusa,” ya kara da cewa.

 

Idan zamu tuna, a ranar Alhamis 5 ga watan Maris ne hukumar ta amince da dage bayyanar sarkin a gabanta har zuwa ranar 9 ga watan Maris.

 

Amma kuma, basaraken wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ne, a ranar Juma’a 6 ga watan Maris, ya mika korafi a gaban kotu a kan hukumar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.