Hukumar ‘yan sandan jihar Niger tayi nasarar kamo wani kasurgumin barawon daya tsere a harin da ‘yan bindiga suka kai gidan kurkukun Kuje.
Hukumar tayi nasarar kama John Ijamu ne a gidansa dake jihar ta Minna bayan ta masu labarinsa.
Yayin da ya bayyana cewa ya dauki tsawon makonni biyu a cikin masallaci kafin ya koma gidan nasa izuwa yanzu da hukuma ta damke shi.
A yau ranar litinin ne hukumar tayi nasarar damke shi, kuma ta kara da cewa zata cigaba da kokari don cigaba da kamo sauran mutanen da suka tsere a gidan yarin.