Babban jami’in dake magana da yawun ‘yan sanda na jihar Zamfara, Shehu Muhammad ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Gummi.
Kuma yace jami’amsu sun kai agajin gaggawa bayan da suka samu labari cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne don su kashe mutane kuma suyi garjuwa dasu.
Inda yace daga bisani maharan sun tsere cikin jeji da raunika kuma sun kashe daya daga cikin su tare da kwace bindigarsa ta Ak 47.