Hukumar ‘yan sandan Najeriya na jihar Ogun tayi nasarar damke wani babban masheki daya tsere a gidan kurkuku na Kuje.
Abdulmumin dan shekara 28 yana cikin mutanen da suka tsere a gidan kurkukun a makon daya gabata bayanda ‘yan bindiga suka kai hari.
Mai magana da yawun hukumar na jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan, inda yace wasu mutane ne suka basu labarin cewa sun ganshi sai suka kama shi.