hukumar ‘yan sandan Najeriya na jihar Adamawa sun damke wani kasutgumin dan ta’addan daya tsere a gidan Kurkukun Kuje.
Dab ta’addan, Abubakar Muhammad dan shekara 23 sun kama shi ne yayin dayake kokarin kokarin tserewa zuwa garin su na Bama dake jihar Borno.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Siriku Akande ya bayyana hakan yayin daya mika shi hannun ‘yan gidan Kurkuku dake jihar a babban birninta wato Yola ranar alhamis.