Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta damke mutane biyu kan mutuwar wani yaro dan shekara uku a wani asibitin dake babban birnin jihar Edo wato Benin.
Mutanen da hukumar ta dama hadda malamar asibitin guda tare da kawunsa Andy Ikoli wanda ya kawo shi asibitin aka ga gawarsa washe gari a wani dakin asinitin.
Mahaifiyar yaron, Mary Ikoli ta nemi a biwa yaron hakkinsa inda tace tana jihar Legas amma ta gaggauta dawowa Benin bayan ta samu wannan mummunan labarin.
Kuma mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar, Chidi ya bayyana cewa suna cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.