fbpx
Monday, August 15
Shadow

Hukumar ‘yan sanda ta damke membobin kungiyar barayi da mashaya guda 42 a jihar Adamawa

Hukumar ‘yan sandan Najeriya dake Zone 3 wanda ke lura da jihar Adamawa da Taraba sun yi nasarar kama masu laifi guda 42 a jihar Adamawa.

Sunan kungiyar masu laifin Shila Boys kuma yawancinsu yara ne matasa wanda aka kama su da kayan shaye shaye da kuma karafunan da suke ta’addanci dasu.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta yankin Yusuf Adamau ne ya bayyanawa manema labarai hakan.

Inda yace sunyi nasarar kama sune bayan mataimakin Inspecta janar, Danjel Sokari Pedro ya kawo masu labarin kan miyagun mutanen.

Leave a Reply

Your email address will not be published.