fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Hukumar ‘yan sanda ta damke wani matashi dayake yaudarar ‘yan mata yana masu sata a jihar Legas

Hukumar ‘yan sanda a jihar Legas ta damke wani matashi dake yaudarar ‘yan mata yanayi masu satar wayoyi da sarkoki.

A ranar asabar ne mai hukumar ta bayyana hakan, inda mai magana da yawunta Hundeyin yace hukumar Surulere suka yi nasarar damke sa.

Yace sun damke shine bayan daya yi nasarar damfarar ‘yan mata sama da talatin da sunan soyyya amma sai ya basu kwaya su sha suyi bacci a Otal yayi masu sata.

A ranar da suka kama shi ya damfari ‘yan mata guda shida inda ya sace masu wayar Iphone 12 guda uku, Iphone 11 guda biyu, tare da sarkoki da kuma gwal wanda farashinsu ya haura miliyan dari biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.