Hukumar ‘yan sanda a jihar Katsina ta bayyana cewa ta gudanar da bincike kan batan naira miliyan 61 a ofishin mai ajiyar kudi na gidan gwamnatin Katsina, Aminu Darma.
‘Yan bindiga ne suka kaiwa Aminu Darma hari suka sace kudin kuma suka harbe shi a hannun.
Inda abokinsa tsohon hadimin gwamnan jihar ta Katsina, Maiwada Danmalam ya bayyana cewa ‘yan bindiga suka kai masa hari bayan ya ciro kudin a baki.
Kuma wani mutun ma yace a gabansa abin ya faru, inda Darma yayi kokarin tserewa amma suka rike masa wuta har motarsa ta kwace masa suka harbe shi suka tafi da kudaden.
Kuma Aminu Darma na asibitin makarantar ‘Yar Adua yana jinya amma anki barin manema labarai su gana da shi.