Wani mazaunin jihar Nasarawa, Tunde Badejo ya kashe mahaifinsa Badejo Idowu kan matsalar da suka samu akan wani filinsu dake karamar hukumar Karu a jihar.
Sun dauke tsawon shekara guda suna jayayya akan cewa shi fa dole sai mahaifin nasa ya bashi wani yanki a cikin filin, amma mahaifin mashi ya bashi hakuri cewa bashi kadai bane keda gadon filin.
Wanda hakan yasa a rigimar da suka yi ta karshe ranar litinin Tunde ya dauki wuka ya caccakawa mahaifin nasa ya aika shi barzahu.
Matar mamacin, Tolanice ta bayyanawa hukuma hakan kuma sun fara neman yaron wanda ya tsere yayin da aka ajiye gawar mahaifin nasa a mucuwari.